• Labaran yau

  May 26, 2017

  Rabin matalauta na duniya na nahiyar Afirka | isyaku.com

  Wani rahoto da aka fitar karkashin Kungiyar Hadin Kai ta Afirka a yayin babban taron raya al’adu da sna’o’in hannu da aka gudanar a birnin Kasabalanca na kasar Morokko ya bayyana cewa, rabin matalauta da ke duniya na a nahiyar Afirka.

  A fadin duniya gaba daya a kwai mutane biliyan 1 da ke fama da yunwa, wato a duk mutum 9 na duniya 1 ba ya samun isasshen abincin da zai ci. Nahiyar Afirka ce ta fi kowacce fama da talauci da yunwa, kamar yadda kwararru suka bayyana. Kwararrun sun ce, rabin matalautan duniya na rayuwa a Afirka.

  Daraktan Kungiyar Hadin Kai ta Afirka Dr. Siyogi Sifa ya jaddada cewa, kaso 41 cikin 100 na talakawan duniya na nahiyar Afirka.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

  wannan labarin ya fara bayyana a shafin TRT
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rabin matalauta na duniya na nahiyar Afirka | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama