Birnin kebbi: New Stars ta ci Kofin Zakarun kwallon kafa,taci Real Flash 5-4 | isyaku.com

An kammala zagayen gasar wasan kwallon kafa na champions league inda aka buga wasan karshe tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Flash da New Stars wanda aka tashi 0-0 bayan Alkalin wasa ya hura usir na karshe a wasan.

Hakan ya haifar da hukuncin cewa a  buga kwallon daga kai sai mai tsaron gida domin a sami zakara a wannan wasan.Bayan amincewar Alkalan wasan da kungiyoyin da abin ya shafa,kungiyoyin sun zabo mutum biyar daga cikin kungiyoyin su domin su buga kwallon na daga kai sai mai tsaron gida na penalty.

Bayan an buga kwallayen na mai tsaron raga Real Flash ta barar da kwallo daya sakamakon sharbe kwallon da mai tsaron gida na  New Stars yayi wanda hakan ya ba kungiyar New Stars nassara a gasar wasan da ci 5-4 kenan.

Bayan an gabatar da kyautuka daga wasu manyan mutane da suka halara a wajen wasan wadanda suka hada da Alh.AC Ladan kwamishinan Filaye da Gidaje na jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar kwallon kafa ta jihar Kebbi da Alh.Hamza Mamuda Maigishiri shugaban kungiyar kwallon kafa na matasa masu tasowa da sauransu.

An mika wa kungiyar New Stars Kofin Zakaru na wasan wanda hakan ya jaddada masu nasarar da suka samu a wannan gasar ta kwallon kafa na karamar hukumar Birnin kebbi.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


Kana sha'awar ka taimaka mana da labarai daga garin da kake domin mu wallafa a ISYAKU.COM? Ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com ko ka aiko sakon SMS kawai zuwa 08062543120

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN