Labaran Duniya a takaice

Fadar shugaban kasar Najeriya ta yi Allah-wadai da sabuwar jita-jitar da ake yaɗawa kan mutuwar Shugaba Muhammadu Buhari, tana mai bayyan...

Fadar shugaban kasar Najeriya ta yi Allah-wadai da sabuwar jita-jitar da ake yaɗawa kan mutuwar Shugaba Muhammadu Buhari, tana mai bayyana hakan da cewa wata manaƙisa ce kawai da ake shiryawa don sanya fargaba a zukatan 'yan ƙasar.

 Kungiyar wasu likitotci na ganawa a Indiya domin yanke hukunci kan ko za a iya zubar da cikin wata yarinya mai shekara 10 da aka yi wa fyade.

A jihar Kano da ke arewa-maso-yammacin Najeriya, makiyaya na kuka da matakan da suke zargin wasu shugabannin kananan hukumomi ke dauka suna sayar da filayen kiwo da buratali ga aminai da magoya bayansu.

Wata ‘yar kunar bakin wake da ke hannun jami’an tsaro ta bayyana yadda Boko Haram suka asirce ta kafin a tura ta harin kunar bakin wake.Yarinyar mai shekaru 14 ta fadawa kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya cewa an zabe ta a cikin masu kai harin ne saboda ta ki yarda ta auri ‘yan Boko Haram din da suka nuna suna son ta.

Wani rahoto da jaridar Sahara Reporters ta wallafa na nuna cewa gwamnan Jahar Zamfara, Abdulazeez Yari ya yi amfani da dala miliyan uku a cikin kudaden tallafi na Paris Club da aka baiwa jahar sa wajen gina Otel a jahar Lagos.Haka kuma an zarge shi da yin amfani da dala miliyan 500 a cikin kudaden wajen biyan wani bashi da ake bin sa.

Kamfanin Tesla ya kaddamar sabon samfurin rufin kwano da ke amfani da hasken rana wajen bayar da wutar lantarki ga gidaje.Shugaban kamfanin, Elon Musk ya bayyana cewa kwanukan sun fi sauran samfuri araha idan aka yi la’akari da kudaden da za a daina kashewa na wutar lantarki.


Wani kwamandan Boko Haram da gwamnati ta yi musaya da ‘yan matan Chibok ya ce nan gaba kadan za su kai hare hare a babban birnin tarayya Abuja, inda a nan ne gwamnatin ta fi bayar da tsaro.
A wani bidiyo da mayakan suka fitar, kwamandan mai suna Abu Darda ya ce ba za su yi wani sulhu ba, kuma gwamnatin ba za ta san kuskuren da ta yi ba wajen sakin su ba sai a lokacin da suka fara kai hare hare.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

COMMENTS

Name

AL-AJABI,25,BIDIYO,1,BIRNIN-KEBBI,26,DUNIYA,23,FADAKARWA,23,FASAHA,3,HOTUNA,40,JAKAR MAGORI,18,LABARI,422,NISHADI,51,SANARWA,13,SHARHI,13,SIYASA,17,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Labaran Duniya a takaice
Labaran Duniya a takaice
https://2.bp.blogspot.com/-H3ghpFABjts/WRm-EChWHqI/AAAAAAAAEpE/xYpP99KY0_UEoYjAzXE1Plrzwq2FQW97gCLcB/s400/bomb3.jpg
https://2.bp.blogspot.com/-H3ghpFABjts/WRm-EChWHqI/AAAAAAAAEpE/xYpP99KY0_UEoYjAzXE1Plrzwq2FQW97gCLcB/s72-c/bomb3.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/05/labarain-duniya-takaice.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/05/labarain-duniya-takaice.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts KARANTA SAURAN LABARAI Karanta saura Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All KARANTA WADANNAN LABEL MAADANI BINCIKA GABADAYAN LABARAI Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy