May 19, 2017

Birnin kebbi:An bizine gawar da aka tsinta,ba'a gane ko waye ba (Hotuna) | isyaku.com

Da misalin karfe 3:10 na rana aka yi wa gawar bawan Allah da aka tsinta a bayan garin Birnin kebbi a shekaran jiya Sallah a cikin wani yanayi man ban tausayi da alhini a harabar dakin ajiye gawa da ke Asibitin Sir Yahaya

Hukumomi a Birnin kebbi sun bayar da umarni domin a bizine gawar wadda ta fara wari domin ta kumbura kuma tana tsiyayar jini.Ala tilas aka gabatar da suturar a haka.

Wasu bayin Allah sun sami halartar Sallar jana'izar gawar kuma daga bisani aka sami mutum hudu da suka bizine shi a makabarta ta hanyar Dukku a garin na Birnin kebbi.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
 


  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
Item Reviewed: Birnin kebbi:An bizine gawar da aka tsinta,ba'a gane ko waye ba (Hotuna) | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba

Raayin mai karatu

Koma Sama