An ga watan Ramadan

Musulmai a kasashe daban-daban na duniya ciki har da Najeriya za su fara azumin watan Ramadan ranar Asabar bayan an sanar da ganin wata.

A najeriya majalisar kolin kasar kan addinin Musulunci ne ta sanar da ganin watan Ramadan din.
Mai alfarma sarkin Musulmi, wanda shi ne shugaban majalisar, Sultan Sa'ad Abubakar III, shi nne ya bayyana ganin watan a garuruwa daban-daban a Najeriya a wani taron manema labarai da aka gudanar a daren Juma'a.

Baya ga Najeriya Musulmai a wasu kasashen duniya irinsu Saudiyya da ma za su fara azumin na watan Ramadana ranar Asabar.

Ramadan dai wata ne mai alfarma ga musulmi inda ake matsa kaimi kan ibada da addu'o'i.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

No comments:

Rubuta ra ayin ka