Dan bautar kasa na NYSC ya mutu a jihar Kebbi | isyaku.com

Wani dan bautar kasa na NYSC Yusuf Ege Olaide,mai lamba  KB/16 A/379, ya rasu ,shugaban hukumar kula da masu bautar kasa NYSC na jiha Alh.Lawal Turai ya shaida haka a yayin bikin rantsar da rukuni na A a sansanin horar da masu bautar kasa a Dakingari ranar Alhamis.


Turawa ya yaba wa Gwamnatin jihar Kebbi bisa wakilai da ta tura Lagos garin mamacin da kudi N500,000 zaman gudunmawa saboda tafiyar da harkokin binne gawar.

Ya kuma kara da cewa masu bautan kasa 2,200 ne aka watsa su zuwa cikin fadin jihar domin gudanar da ayyukan bautan kasa,ya kuma nuna gamsuwa da yadda matasan suka fahinci horon da aka yi masu.@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN