April 24, 2017

Gwamnatin jihar kebbi ta nada kwamitin bincike akan jaririn da aka yankewa hannu a asibitin Zuru.

Gwamnatin jihar kebbi ta nada wannan kwamitin domin yin kwakwaran bincike akan faifan Bidiyo da ake ya dawa a kafa fen Sada zumunta na zamani,mai dauke da hoton jaririyar da aka yankewa hannu tun a cikin, cikin mahaifiyar ta, bayanda aka kai mahaifiyar asibitin gwamnati dake garin zuru anan jihar kebbi.

Gwamnan jihar kebbi sanata Abubakar Atiku Bagudu ne ya nada wannan kwamitin nan take bayan ya kalli tattaunawa da akayi da dan'uwan mijin matar da ta haifi jinjirar, da yammacin lahadi 23/04/2017.

Kwamitin dai ya kunshi kwararrun likitoci ,lauyoyi da kuma jami'an tsaro domin su bankado gaskiyar lamara domin daukan matakin da ya dace, da kuma magance aukuwar irin wannan matsalar a gaba.

Da yake jawabi Jim kadan bayan kammala nada kwamitin, gwamna Bagudu ya bada tabbacin daukan duk wani mataki da yadace akan wannan matsalar,"Babu shakka hakken kowace gwamnati ne ta kare mutunci da hakken al'ummar da take jagoranta da kuma dukiyoyin su,"inji shi, tare da nuna alhininsa akan hoton da ya gani na wannan jinjirar.

Aisha Augie-Kuta
Mataimakiya,ta musamnan
Akan kafar zamani ta yanar gizo.
Ga gwamnan Jihar kebbi.


@ISYAKUWEB KU BIYO MU A SHAFIN MU NA FACEBOOK
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
Item Reviewed: Gwamnatin jihar kebbi ta nada kwamitin bincike akan jaririn da aka yankewa hannu a asibitin Zuru. Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
Koma Sama