An kama wani Mutum da sassan bil'adama a Ilori

An kama wani mutum mai matsakaitan shekaru da mallakar wasu sassa na jikin bil'adama a garin Ilori babban birnin jihar Kwara.

Jaridar Tribune ta labarta cewa mazauna Ita Kudim,Abata Suban yankin Pakata na karamar hukumar Ilori ta kudu sun dade suna sa ido akan harkar wannan mutum wanda ya haifar da jita-jita cewa mutumin ya mallaki wata gawa.

Daga bisani makwabtan mutumin sun afka cikin gidan da mutumin yake inda suka tarar da gawa da kuma wasu sassa na jikin bil'adama a cikin gidan.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kwara Mr Olusola Amore ya shaida faruwar haka ga manema labaru amma bai fadi sunan mutumin da ake zargin ba.

Sashen binciken laifukka na CID a hukumar ta 'yan sandan jihar tana ci gaba da bincike akan lamarin.

@isyakuweb  ku biyo mu a shafin mu na Facebook


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN