Gwamnati ta daukaka kara,ta kuma sake sabunta tuhuma akan Justice Ademola

Rahotanni daga birnin Abuja sun nuna cewa Gwamnatin tarayya ta daukaka kara akan hukuncin da Maishari'a Justice Jude Okeke ya yanke akan karar da Gwamnati ta shigar akan Justice Adeniyi Ademola, Olabowale Ademola da Joe Agi.

Majiyarmu ta labarta mana cewa Gwamnati tayi hakane domin ta kare martabar tsari na yaki da cin hanci da rashawa,rahotannin sun kara da cewa Gwamnatin tarayya ta hannun ofishin ma'aikatar shari'a ta kasa ta sake shigar da kara akan Alkalan,wannan karo a bisa zargin cewa suna rayuwa da kudade da suka fi karfin abin da Gwamnati take biyan su tare da yin karya wajen bayyana kadarorin su ga hukumar da abin ya shafa.

Justice Jude Okeke dai ya sallami Alkalan da hukumomi suka gurfanar da farko akan laifin cin hanci da rashawa a bisa dalilai da yace na rashin cikar da'awa ta hanyar kasa gabatar da sahihin laifin da ake zargin su da shi wanda bangaren masu shigar da kara suka kasa gabatarwa.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
ya wanke su daga zargin da ake yi masu.
Gwamnati ta daukaka kara,ta kuma sake sabunta tuhuma akan Justice Ademola Gwamnati ta daukaka kara,ta kuma sake sabunta tuhuma akan Justice Ademola Reviewed by on April 09, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.