Mai girma Galadiman
Zuru Sen. Maj. Gen. Muhammadu Magoro OFR ya nemi aduba ma kasar Zuru hanyar da
ta taso daga Gadar zaima zuwa Gamji. Sen. Magoro yayi wannan koken ne acikin jawabinsa
na godiya bayan kammala Uholar bana. Ya kara dacewa wannan hanya da ta taso daga
iyakar Jihar Zamfara da Kebbi ta biyo ta cikin Masarautar Zuru takare a iyakar Jihar
Kebbi da Niger ta zama babbar kalubale ga mutanen Kasar Zuru da kewaye.
Duk da yake wannan
hanya ta Gwamnatin Tarayyace amma anyi kokarin sanya Gwamnatin Jiha ta gyarata daga
baya Gwamnatin Tarayya ta biya amma sai akayi rashinsa’ar Gwamnatin Tarayya ta
dakatarda Gwamnatocin Jahohi dayin aikin Gwamnatin Tarayya don antara mata bashi
sai ta gama tantancewa. Don haka yake kira ga Wakilin Shugaban Kasa a wurin bukin
wato Maigirma Ministan Matasa da Wasanni Barr. Solomon Dalong (Sodangin Zuru)
da aduba wannan matsalar.
A nasa jawabi
Maigirma Ministan Wasanni da Matasa Barr. Solomon Dalong yayi alkawalin zai nemi damar da shi da Sanata Bala
Ibn – Na’Allah da kuma Galadiman Zuru zasu zauna da Maigirma Shugaban Kasar Najeriya
Muhammadu Buhari don tattaunawa akan wannan matsala da sauran matsaloli.