Buhari na iya ci-gaba da aiki da Magu-Falana

Babban lauya Femi Falana, ya ce kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba shugaba Buhari karfin ikon ci-gaba da aiki da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC har illa-masha-Allahu.

Falana, ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabi a cikin shirin Sun Rise Daily da gidan talabijin na Chanels ke shiryawa, inda ya ce ba daidai ba ne a ce Magu ba zai iya ci-gaba da aiki ba don kawai majalisar dattawa ta ki tantance shi.

Lauyan ya kara da cewa, kamar yadda ya ke a sashe na 171 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, akwai nade-naden da ba su bukatar shugaban kasa ya nemi amincewar wani.

Ya ce ‘yan majalisa su na da ‘yancin tantance jakadu da sauran hukumomin harkokin ketare ne kawai, kamar yadda ya ke kunshe a sashe na 171 sakin layi na 2 na kundin tsarin mulkin Nijeriya.


Liberty

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
Buhari na iya ci-gaba da aiki da Magu-Falana Buhari na iya ci-gaba da aiki da Magu-Falana Reviewed by on April 03, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.