Birnin kebbi: Mota ta kashe jami'in FRSC akan titin Ahmadu Bello

Da safiyar yau Litinin da misalin 11:30 na safe a titin Ahmadu Bello bayan an wuce randabawal na Asibitin Sir Yahaya a garin Birnin kebbi wata mota ta buge wani jami'in hukumar kare hadurra ta kasa FRSC wanda ke bakin aiki,lamarin da ya haifar da mutuwar jami'in mai suna Babangida Muhammed nan take,shi kuma direban motar yaki tsayawa.

Majiyarmu wanda ganau ne ba jiyau ba ya tabbata mana cewa motar tana tafiya a kimanin mita 150 daga randabawal na Sir Yahaya wajen da jami'an ke sintiri akan titi sai direban ya tuko motar a guje,su kuma jami'an suka yi tsalle domin su bayar da hanya domin motar ta wuce,garin haka ne motar ta buge Babangida wanda kanshi ya bugi dutsen tsakiyar kwalta wanda ya haifar da zubar jini a hanci,kunne da buma baki.

Ganin hakan ne yasa jami'an na FRSC suka zagaya da Babangida cikin gaggawa zuwa Asibitin Sir Yahaya inda likata da bayason a fadi sunansa ya tabbatar da rasuwarsa,ya ce a lokacin da aka shigo da Babangida rai yariga yayi halin sa.

An riga anyi jana'iza kamar yadda addinin Musulunci yayi umarni.Yayan marigayi Babangida watau Nura Muhammed wanda shine Hakimin kokuma Mai unguwar Nassara2 a garin Birnin kebbi,yayi wa kanensa kyakkyawar addu'a don Allah ya kai rahama a kushewar kanensa.Ya kuma roki hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da adalci a cikin binciken da  suke yi akan lamarin.

A yayin da ISYAKU.COM ya tuntubi kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Kebbi DSP Mustapha Muhammed ya tabbatar da aukuwar lamarin haka kuma mutuwar jami'in,ya kuma gaya mana cewa an kama direban da ya buge jami'in FRSC din kuma yana amsa tambayoyi daga jami'an 'yan sanda a garin Birnin kebbi.Wata majiya kuma ta tabbatar mana cewa an kama direban ne a garin Kalgo kilomita 12 daga garin Birnin kebbi.@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN