Bashin Manoma: Gwamnati zata gurfanar da manoma da basu biya bashi ba a Kotu

Gwamnatin jihar Kebbi ta ba manoma da suka amfana da bashi da Bankin manoma ya bayar a karamar hukumar mulki ta Suru mako uku su biya kudaden bashin da suka karba ko su fuskanci gurfana a gaban Kotu.

Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa kimanin manoma 11,000 ne suka amfana da N128,200 kowannen su a karkashin shirin da zasu samar da shinkafa da alkama ta hanyar noma.

A yayin da yake jawabi a garin Suru Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban kwamitin karban kudaden bashin daga manoma Col. Samaila Dabai Yombe ya bayyana wa manoman cewa Manoman da basu biya kudaden bashin ba kafin 10 ga watan Juli zasu fuskanci tuhuma ta hanyar gurfana a gaban kotu akan zancen bashin.

Kantomar karamar hukumar ta Suru Alh.Umar Mai gandi da Sarkin Suru Dr. Muhammad Bello sun roki Gwamnatin jihar Kebbi da Bankin Manoma akan cewa su kara ba Manoman Mako uku domin su biya bashin.

@ISYAKUWEB   https://web.facebook.com/isyakuweb

Bashin Manoma: Gwamnati zata gurfanar da manoma da basu biya bashi ba a Kotu Bashin Manoma: Gwamnati zata gurfanar da manoma da basu biya bashi ba a Kotu Reviewed by on April 21, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.