• Labaran yau

  March 14, 2017

  Soja ya kashe wata macen soja a kan zargin soyayya da wani


  Wani sojan sama na Najeriya ya harbe abokiyar aikinsa itama sojar sama a wuya har lahira a bisa zargin cewa tana soyayya da wani mutum daban bayan shi.Sojan da ya aikata wannan laifi mai suna Kalu M.O ya fada hannun 'yan sandan sojan sama a barikin sojan sama da ke Makurdi a jihar Benue inda ake tsare da shi a bisa tuhumarsa da laifin kisan Macen sojan sama mai suna Sholape.

  Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da karfe 4:36 na asuba a dakin wanda yayi kisan watau Kalu,kuma ita mariganyar ta kwana a dakin Kalu ne a ranar da abun ya faru saboda dama can budurwar shi ce da suka fara soyayya tun 2016.Bayanai sun nuna cewa Kalu yayi yunkuri domin ya kashe kanshi har ma ya rubuta takardar alamar cewa zai kashe kanshi amma sai ya kasa.


  Wata majiya ta shaida wa ISYAKU.COM cewa idan aka sami Kalu da laifin kashe Mace sojan sama abokiyar aikin shi to lallai zai fuskanci hukuncin kisa ne ta hanyar daure shi a durom kuma a harbe shi har lahira shima.Wannan shari'ar dai Kotun musamman ta soja ce zata aiwatar da shi.

  Isyaku Garba
  @isyakuweb kubiyo mu a facebook
  https://web.facebook.com/isyakuweb
  Aiko da Labari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Soja ya kashe wata macen soja a kan zargin soyayya da wani Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama