Jaiz-Bankin Musulunci, "Ba ma fuskantar durkushewa domin rashin Kostomomi"


A ‘yan shekarun baya da suka wuce  musamman daga 2012 zuwa 2013 aka dinga samun sakonnin musamman a shafukan sada zumunta na whatsapp,twitter da facebook kai harma da sakonni na sms wanda a cikin sakonnin ana bukatar wai mutane su ziyyarci bankin musulunci  ta Jaiz su buda asusun ajiya domin a ceci bankin ta Jaiz daga barazanar durkushewa wanda take fuskanta saboda rashin kostoma masu hulda da bankin.

Wannan irin sakonnin sun sake bullowa kuma a whatsapp da kuma facebook,dauke da sakon cewa bankin Jaiz tana kan hanyar durkushewa saboda rashin kostoma masu buda asusun ajiya a bankin.A bisa wannan tubalin ne ISYAKU.COM ta bi diddigi domin ta gano gaskiyar ko me ke faruwa ne akan wannan zancen da yake yawatawa a shafukan sada zumunta game da bankin musulunci ta Jaiz.

A yayin da muka tuntubi babban ofishin bankin Jaiz ta kasa game da wannan batun,wata wakiliyar bankin wanda bata son a fadi sunanta ta tabbatar mana da cewa duk wadannan sakonnin da ke zagayawa game da bankin ba gaskiya bane kuma ba bankin ne ya aika wannan sakonnin ba.Ta kuma kara da cewa tuni bankin ta Jaiz ta nisanta kanta daga wannan sakonnin,jami’ar ta ce suna samun karuwar sababbin masu buda asusun ajiya a bankin da kuma hulda da bankin Jaiz a ko da yaushe saboda haka ba gaskiya bane cewa bankin na fuskantar barazanar durkushewa saboda rashin masu hulda da bankin.

A ziyarar gani wa ido da ISYAKU.COM ta kai a reshen bankin na Jaiz da ke garin Birnin Kebbi,mun gani ana hada-hada da jama’a kamar yadda kowane banki na zamani ke yi,kowane ma’aikaci yana kan aikinsa haka kuma jami’an tsaro na bankin suna kan aiki kamar yadda kowane banki ke gudanar da ayyukan ta a kasarnan.

Isyaku Garba
@isyakuweb  Ku biyo mu a Facebook

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN