Labarai a takaice 26/3/2017

Gwamnatin Mali ta ce taron kasa da ta shirya na fahimtar juna na nan kamar yadda aka shirya a gobe litinin duk da wani bangare na jam&...


Gwamnatin Mali ta ce taron kasa da ta shirya na fahimtar juna na nan kamar yadda aka shirya a gobe litinin duk da wani bangare na jam'iyyun adawa da kuma ‘yan tawayen kasar sun ce zasu kauracewa taron.
Gwamnatin Mali tace ta shirya wa taron wanda Za a share tsawon mako daya ana gudanarwa daga gobe Litinin zuwa 2 ga Afrilu.
Amma wasu jam’iyyun adawa da ‘yan tawayen sun ce zasu kauracewa taron wanda aka shirya karkashin yarjejeniyar da aka cim ma a Algiers a 2015.
Amma bangaren ‘yan tawayen MAA da ke fafutikar kafa kasar Azawad sun ce zasu ahalarci taron.
Taron na fahimtar juna ya shafi yin muhawara game da rikicin kasar tsakanin bangarori da dama da nufin sasantawa da kuma zaman lafiya.
Wasu jam’iyyun adawa na son a shafe makwanni ana taron maimakon mako guda.
A shekarar 2012 ne ‘yan tawaye suka kwace ikon arewacin Mali, kafin dakarun Faransa fatattake su a 2013.
Amma har yanzu an kasa wanzar da zaman lafiya a Mali.


Likitoci a kasar Japan sun bukaci mutanen da ke yawan tashi da daddare domin yin fitsari da su rage shan gishiri a abinci idan suna so su daina yawan tashi.
Matsalar yawan tashin fitsarin dare - wacce ta fi addabar mutanen da suka haura shekara 60, tana hana mutum samun bacci mai dadi sannan tana yin illa ga rayuwar mutanen.
Wani bincike da likitoci suka gudanar kan mutum 300, ya gano cewa rage shan gishiri a abinci yana sanya wa mutane su rage yawan tashi yin fitsarin dare.
Likitocin na Jami'ar Nagasaki sun fitar da sakamakon bincikensu ne a wurin taro na kungiyar kula da mafitsara ta Turai da aka yi a Landan.
Sun bibiyi mutanen da ke shan gishiri sosai da kuma matsalar rashin bacci tsawon wata uku, bayan sun ba su shawara su rage shan gishirin.
Binciken ya nuna cewa sun rage zuwa fitsarin dare daga sau biyu zuwa sau daya.
Baya ga haka, binciken ya nuna cewa mutanen da suka rage shan gishirin da rana ma sun daina yawan zuwa fitsar sannan rayuwarsu ta inganta.
Matsalar yawan tashi yin fitsari da daddare ta fi samun mutane - maza da mata- da suka manyanta.


Yayin da darajar Naira ke ci gaba da farfadowa a kaswannin canji a fadin kasar nan, tuni cikin da yawa daga cikin yan kasuwar canjin ya fara durar ruwa.
Wannan ya biyo bayan zuba dala miliyan 100 da babban bankin Nijeriya ya yi a ranar Alhamis din da ta gabata a kasuwannin.
Biyo bayan haka ne aka fara sayarda da dalar akan Naira 385 a kasuwannin canjin a babban birnin tarayya Abuja, yayin da ake sayar da dalar akan naira N400 a jahar Lagos.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa canji Ahaji Aminu Gwadabe ya bayyanawa manema labarai cewa cikin ‘yan kaswuar ya duru ruwa saboda suna sayen dala ne akan naira 381 daga hannun baban bankin Nijeriya, inda su kuma aka umarce su da su sayar akan naira 399.
Ya ce sai gashi an sayar da dalar har a N385, al’amarin da ya sa masu saya su kan kafewa akan sayen dalar akan wannan farashi
Ya kara da cewa, baya da kudaden da babban bankin ya zuba, da yawa a cikin wadanda suka boye dalar sun fito da ita domin su sayar, gudun kar su tafka mummunar asara ya ce ana sayen dalar a hannun wadannan mutane akan naira N380 saboda kowa ya san cewa boye dalolin suka yi.

@isyakuweb--Shafin mu na Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb

 

COMMENTS

Name

AL-AJABI,25,BIDIYO,1,BIRNIN-KEBBI,26,DUNIYA,23,FADAKARWA,23,FASAHA,3,HOTUNA,40,JAKAR MAGORI,18,LABARI,422,NISHADI,51,SANARWA,13,SHARHI,13,SIYASA,17,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Labarai a takaice 26/3/2017
Labarai a takaice 26/3/2017
https://1.bp.blogspot.com/-g2AkYwpQCw4/WNfx5sEtLeI/AAAAAAAADto/pQgenoa-kkk2ABoKjGIDs_4vNeRwuAOhgCLcB/s320/1000-naira-notes.jpg
https://1.bp.blogspot.com/-g2AkYwpQCw4/WNfx5sEtLeI/AAAAAAAADto/pQgenoa-kkk2ABoKjGIDs_4vNeRwuAOhgCLcB/s72-c/1000-naira-notes.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/03/labarai-takaice-2632017.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/03/labarai-takaice-2632017.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts KARANTA SAURAN LABARAI Karanta saura Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All KARANTA WADANNAN LABEL MAADANI BINCIKA GABADAYAN LABARAI Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy