Kotu Ta Bada Umarnin a Kama Jikan Marigayi Ahmadu Bello, Magajin Garin Sokoto

Wata kotu a jahar Sokoto ta bada umarnin a kama Magajin Garin Sokoto, Alh. Hassan Danbaba wanda jika ne ga marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto.
Wannan ya biyo bayan wata kara da Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na yankin Arewa Maso Yamma Inuwa Abdulkadir ya shigar a gabanta, inda ya ke bukatar a bi masa hakkinsa akan cin zarafin da Magajin Garin Sokoton ya yi masa.

Abdulkadir ya fadawa kotun yadda Magajin Garin Sokoton ya masa kazafin cewa wai ubansa bawa ne wanda wata mata mai suna Goggo ta siya akan sile biyu a wancan zamanin.
A don haka ne Lauyan mai kara ya roki kotu da ta umurci Sifeto Janar din ‘yan sanda Idris Ibrahim da ya kamo Magajin Garin Sokoto a duk inda yake.

Alkalin kotun ya amince da wannan bukata, sai dai kwamishinan ‘yan sandan jahar Sokoto aka umarta da ya kama shi ba Sifeto janar ba.

Za a ci gaba da sauraran karar a ranar 6 ga watan Afrilu.(Mujallarmu)
@isyakuweb--Ku biyo mu a shafin mu na Facebook
https://web.facebook.comPost a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN