Guba da aka sanya wa shugaba Buhari,Kuskuren farko laifin waye ? (1)

Akwai rade radin da ke zagayawa a wasu kafafen watsa labarai na yanar gizo musamman shafukan sada zumunta irin su Twitter,Facebook da ...Akwai rade radin da ke zagayawa a wasu kafafen watsa labarai na yanar gizo musamman shafukan sada zumunta irin su Twitter,Facebook da sauran su cewa Fadar shugaban kasar Najeriya ta gayyato tsohon Dogarin marigayi Janar Abacha domin ya kasance a cikin tawagar wasu gayyatattun kwararrun masana akan harkar tsaro da aka gayyato domin su bincika yadda aka bari har aka sanya guba a cikin tukunyar iskan gas na na'urar sanyaya daki na dakin shugaban kasa wanda hakan yayi sanadin rashin lafiyar da shugaban kasa yayi fama da shi.

Da farko dai sharhin mu zai ta'allaka ne akan kuskuren da aka yi tun farko wajen tafiyar da tsarin tsaron fadar shugaban kasa wanda hakan ne ya haifar da gibin da aka sami damar da aka aikata wannan mummunar aiki da sakamakon shi zai iya haifar da mummunat zubar da jinin da nahiyar Afirka bata taba ganin irin shi ba,da ace ta Allah ta kasance akan shugaba Buhari kuma ya bayyana cewa guba ne aka saya mashi.

Bayan da shugaban kasa ya karbi mulki daga shuga Jonathan,shugaban hukumar ayyukan asiri da tsaro ta DSS Mr.Itah a wancan lokacin ya nada wasu dogarawa na tsaron fadar shugaban kasa a daidai lokacin da yake shirin barin ofishinsa saboda canjin shugabanci na kasa.Wannan bai kamata ba kuma baya cikin tsari,sabon darakta janar na hukumar ayyukan asiri da tsaro ta kasa karkashin sabon shugaban kasa shi ne ya kamata ya nada dogarawan tsaron lafiyar shugaban kasa.

Bayan da Buhari ya tare a cikin fadar shugaban kasa,hukumar ayyukan asiri na soja da ake kira NAIC (Nigerian Army Intelligence Corps) sun mamaye fadar shugaban kasa da sunan tsaron lafiyar shugaban kasa.Aikin NAIC a hukumance shine tattatara bayanai ta hanyar leken asiri akan harkokin Soja da ababen da suka shafi tsaro da ya shafi aikin Soja.

DSS kuma a hukumance ita ke da hakkin kare lafiyar shugan kasa da na iyalin shi,haka Gwamnoni da shugaban Majalisan dattijai da na wakilai da kakakin Majalisa na jihohi.A ko ina a kasashen da suka ci gaba a Duniya ,hukumomin ayyukan asiri,ko na leken asiri kamar su Secret Service na kasar Amurka,B15 na kasar Ingila,Musad na Isra'ila da sauran su ,su ke tsaron lafiyar shugabannin kasashensu.

An sami jayayya akan ko waye zai jagoranci tsaron lafiyar shugaba Buhari a lokacin da ya shigo fadar shugaban kasa a tsakanin hukumar Soja wanda take ganin shugaba Buhari tsohon Janar ne saboda haka ita ke da hurumin kare lafiyar shi saboda haka aka aika dakaru na NAIC suka ajiye Kaki suka sanya Kwat da bakin madubi suka shiga tsaron lafiyar shugaban kasa.

A tsarin kare lafiyar shugaban kasa akwai tsari da ake kira zobe na tsakiya,wannan yana nufin dakarun tsaro na kusa da shugaban kasa wanda ke da takamammen aiki da zasu yi a kullum a bisa horo,haka kuma akwai tsari na matakai har kashi bakwai na tsaron lafiyar shugaban kasa wanda DSS kadai ne ke da irin wannan horon a cikin hukumomin tsaro na Najeriya domin huruminta ne.

Bayan da dakaru na NAIC suka kama aiki a fadar shugaban kasa,DSS sun kasance tare da su,amma zama ne na kasanni na sanka,kowa yana bin umarnin uban gidanshi ne,ka gani dole tun farko a fami matsala,duk da yake akwai babban dogari na dogarawa masu aikin tsaron fadar shugaban kasa da ake kira CSO.

Rinjayen jami'an NAIC basu je suka sami horo na tsaron lafiyar shugaban kasa ba a kafin aka tura su zuwa fadar ta shugaban kasa.Amma babu wanda DSS zata tura shi fadar shugaban kasa matsawar bai je ya sami horo (course) na tsaron lafiyar manyan mutane ba wanda shima wani darasi ne na kashin kanshin da ake koyarwa a makarantar ta DSS da ake kira DSS Academy.

Ku kiyo mu a kashi na 2 don ci gaba......


@isyakuweb--Ku biyo mu a shafin mu na Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb

COMMENTS

Name

AL-AJABI,25,BIDIYO,1,BIRNIN-KEBBI,26,DUNIYA,23,FADAKARWA,23,FASAHA,3,HOTUNA,41,JAKAR MAGORI,20,LABARI,426,NISHADI,51,SANARWA,13,SHARHI,13,SIYASA,17,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Guba da aka sanya wa shugaba Buhari,Kuskuren farko laifin waye ? (1)
Guba da aka sanya wa shugaba Buhari,Kuskuren farko laifin waye ? (1)
https://3.bp.blogspot.com/--cY2KA5xjrY/WNgzove0Z5I/AAAAAAAADuU/tnkRxol4WJkMFYhqxydEtqTyvZppAzoZgCLcB/s320/army.PNG
https://3.bp.blogspot.com/--cY2KA5xjrY/WNgzove0Z5I/AAAAAAAADuU/tnkRxol4WJkMFYhqxydEtqTyvZppAzoZgCLcB/s72-c/army.PNG
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/03/guba-da-aka-sanya-wa-shugaba.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/03/guba-da-aka-sanya-wa-shugaba.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts KARANTA SAURAN LABARAI Karanta saura Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All KARANTA WADANNAN LABEL MAADANI BINCIKA GABADAYAN LABARAI Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy