'Yan sanda sun kama N111.3 Miliyan na zargin cin hanci a Jihar Rivers


Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta gano N111.3 Miliyan daga wajen Kwamishinonin zabe da suka gudanar da zaben da aka kammala a Jihar Rivers ran December 10,2016.  Sun kuma yi zargin cewa N360 Miliyan ne Gwamna Nyesom Wike ya bayar a matsayin na goro ga jami'an hukumar zabe da suka gudanar da aikin zaben.
'Yan sandan sun yi zargin cewa kudaden wani cin hanci ne da Gwamna Nyesom Wike ya bai wa Kwamishinonin zaben da wasu jami'an tsaro domin su tafka magudi a zaben.
Wasu jami'an 'yan sanda su shida da aka samu da hannu a wannan badakalar an kore su daga aikin 'yan sanda kuma za'a gurfanar da su a gaban Kotu .Gwamna Wike ya karyata akata ba dai dai ba.

'Yan sanda sun kama N111.3 Miliyan na zargin cin hanci a Jihar Rivers 'Yan sanda sun kama N111.3 Miliyan na zargin cin hanci a Jihar Rivers Reviewed by on February 08, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.