An hana sa kaya matsattsu a Legas


Jami'ar Lagos da ke Najeriya ta haramta wa maza da mata sanya tufafin da ke matse jiki, sannan ya fito da surar jikin nasu.
Wata sanarwa da jami'ar ta fitar, wadda kafofin watsa labaran kasar suka ambato, ta ce tufafin da aka hana sanya wa sun hada da matsattsun turoza da sket da bulawus.
Hukumomin jami'ar sun kuma haramta sanya "duk wasu tufafi da ke nuna tsaraicin mutum da suka hada da nuna kirji da ciki da ƙasan cinya da katara ko duwawu".
Sanarwar ta bukaci dalibai su "rika yin shiga ta kamala a cikin jami'a. Sanya tufafin da ke matse jiki da rigunan da ba su da madaurin kafada da kuma wadanda ke nuna al'aura ba su dace ba."
BBCHausa

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. A gaskiya wanga matakin da anka dauka a lagas dai dai na,wayanga matan dadewa sunka yi suna cin amanar idadunan mu saboda sa tufafi da sukai mai nuna tsiraici su.kai kuma isyaka seniora all ya saka ma.naji ance wasu wulakantattun yara su ci zarafin ka don ka taimaka masu,halin wasun mu na na birnin kebbi,ka yi hakuri ba mu da irin ka walla a nan birnin kebbi.abin da ba a yi ba kai kayyi mana.don kai dai ka bada labarin garin birnin kebbo.godiya mukai wallah,duk kazafi,sheri ku mugunta da aka yi ma rokon ka mukai kayi hakuri.


    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN