Shugaba Buhari Ya Tsawaita Hutun Da Ya Ke Yi a London

Shugaban Muhammadu Buhari ya kara wa’adin hutun da ya dauka wanda ya ke yi a birnin London da ke kasar Ingila.
Wannan ya na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Adesina ya ce shugaban ya rubuta wa majalisa takardar neman tsawaita wa’adin hutu nasa domin ya samu damar yin gwaje gwaje da likitocin sa suka umarce shi ya yi.
Shugaba Buhari dai ya dauki hutun ne a ranar 19 ga watan Janairu, kuma a gobe Litinin, 6 ga watan Fabrilu ne ya kamata ya dawo gida Nijeriya. Toh sai dai sanarwar ba ta bayyana adadin ranakun da zai tsawaita hutun da su ba.
MUJALLARMU
Shugaba Buhari Ya Tsawaita Hutun Da Ya Ke Yi a London Shugaba Buhari Ya Tsawaita Hutun Da Ya Ke Yi a London Reviewed by on February 05, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.