• Labaran yau

  February 27, 2017

  Ki rama idan Mijin ki ya mare ki - Sarkin Kano

  Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya umarci Diyar shi akan cewa ta rama matukar Mijin ta ya mare ta.Wannan ya biyo bayan jawabi ne da ya yi a lokacin da aka daura wa Zawarawa 1500 Aure wadda Gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyi.Mai Martaba Sarki Sanusi ya nuna damuwar sa akan yawan koke-koken tashin hankali a tsakanin Magidanta inda lamarin  ke kaiwa har ga duka da Maigida ke likida wa Matar sa.

  Sarkin ya kuma kara da cewa duk wani mai sarautar gargajiya a kasar Kano Hakimi,Dagaci ko wani Mai Rawani na Sarauta da aka samu da laifin cewa ya mari Matar shi,tau lallai a bakin rawanin sa.

  Isyaku Garba-Birnin kebbi
  @isyakuweb Ku biyo mu a Facebook
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ki rama idan Mijin ki ya mare ki - Sarkin Kano Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama