• Labaran yau

  February 16, 2017

  Kotu ta kwace Naira Biliyan 34 na Tsohuwar Ministan mai na Najeriya

  Wata babbar Kotu a garin Lagos karkashin shugabancin Alkalin Kotun Mai shra'a (Justice) Muslim Hassan ta kwace kana ta halatta wa Gwamnatin tarayyar Najeriya Naira Biliyan 34 mallakin tsohuwar Ministan man fetur na Najeriya karkashin tsohuwar Gwamnatin Goodluck Jonathan Mrs Diezani Alison-Madueke.

  Hukumar kama masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'arnaki ta EFCC ce ta shigar da karar kuma ta bukaci Kotun ta kwace kudaden wanda bayan gabatar da shedu da cika matakai na shara'a,Kotu ta yanke hukuncin mika kudaden ga Gwamnatin tarayya.


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta kwace Naira Biliyan 34 na Tsohuwar Ministan mai na Najeriya Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama