• Labaran yau

  Wata Mata ta kai kara a Kotu domin an ki a kashe ta

  Wata Mata a garin Taquatinga na kasar Brazil ta kai karan wani mutum a Kotu domin a cewar ta ,ta biya shi wasu kudade masu yawa wanda ba'a fadi ko nawa bane domin ya kashe ta amma shi Mutumin wanda shi ma ba'a fadi sunan sa ba ya kasa cika alkawarin kwantiragin da matar ta ba shi domin ya kashe ta.

  Ita dai wannan Macen,bayanai sun nuna cewa ta yi fama da cutar matsanancin damuwa (depression) kuma tayi yunkuri domin ta halaka kan ta a lokuttan baya amma ba tare da ta sami nassara ba.Wannan dalilin ne ya sa ta dau hayan wani mutum mai kashe mutane kuma ta biya shi domin ya kashe ta, bayan ta bashi makuddan kudi ta kuma ba shi motar ta .Amma mutumin bai kashe ta ba wanda yin hakan ya harzuka matar ita kuma ta garzaya zuwa kotu.

  Bayan matar ta shigar da kara a kotun garin Taquatinga,Alkalin Kotun ya baiyana mata cewa tun asali ita wannan kwangila haramtacciya ce kuma baya cikin tsari.Daga karshe dai Alkalin Kotun ya kori karar da Matar ta shigar a gaban wannan Kotun.

  Daga Isyaku Garba-Birnin kebbi


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wata Mata ta kai kara a Kotu domin an ki a kashe ta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });