• Labaran yau

  February 07, 2017

  Karuwa ta zama Minista a wata Kasa


  Wata Minista a Kasar Zimbabwe ta nemi ‘Yan Kasar su bar tuna lokacin baya, Ministar dai ta taba zaman kan-ta a baya, tace amma yanzu ai komai ya wuce, kuma kyaun ta a dai bar tuna baya.

  Minista Kampamba Mulenga ta yada labarai a Kasar Zimbabwe tace abin da za ayi la’akari da shi yanzu shine aikin ta a matsayin Ministan yada labarai. Ministar tace yanzu ta canza ta kuma ajiye wancan aiki a gefe.

  Ministar tayi wannan magana ne inda ta ke nuna takaicin ta da wasu da ke kiran ta da sunan da aka san ta a da. Kampamba Mulenga ta cewa Mutanen Kasar yanzu ta canza ya kamata kuma al’umma su ba ta girman ta. Kafin ta zama Minista a Gwamnati dai kamar yadda Daily Post ta rahoto kowa ya san ta a matsayin mai zaman kan ta.

  A farkon wannan Watan tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya gabatar da jawabi a gaban Majalisar Amurka inda aka gayyace sa domin yayi magana game da matsalolin Najeriya musamman rikicin addini da sauran su.
  NAIJ.COM
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karuwa ta zama Minista a wata Kasa Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama