• Labaran yau

  “A shirye muke Arewa ta ɓalle daga Najeriya” – Farfesa Ango Abdullahi


  Farfesan Ango Abdullahi ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da yayi da jaridar Sunday Sun, inda yace Arewa bata tsoron a raba Najeriya, har ma ya kara da bada shawarar yadda za’a yi wajen raba Najeriyar, day ace kamata yayi a kira wani babban taro, wanda za’a bashi karfin raba Najeriyan.

  Ango Abdullahi yace idan yan Najeriya sun ga damar zama da junansu cikin lafiya da girmamawa toh shikenan, ba matsala. Amma idan yan Najeriya suka nuna sha’awar a raba kasar ta bangarorin addinai ko kabilu, toh ai sa a raba kowa a bashi kasonsa. “duk wanda ya fada maka cewar dayawa daga cikin mutanen Arewa basa son a raba Najeriya karya yake yi.” Inji Ango Abdullahi.

  KU KARANTA: Zaman lafiya yafi zama ɗan Sarki: Za’a sulhunta rikicin kudancin Kaduna

  Dayake karin haske game da shirin Arewa na ballewa daga Najeriya, Ango Abdullahi yace “tabbas a shirye muke mu kama gaban mu idan an raba Najeriya, abinda ya rage kawai shine mu ga yadda za’a raba. Shekaruna a yau 78, kuma na samu damar halartan jami’ar kwaya daya tilo dake Najeriya a wannan lokacin, wato jami’ar Ibadan, babu wanda zai fada min tarihin Najeriya wanda ban sani ba.

  Ina sane da abubuwa masu tarin yawa, saboda kusan a gabana akayi komai, da girmana aka yi su. mutanen da suka yi ta fafutikan ganin an samar da jihohi a shekarun 1966/1967 sune kuma a yau ke kira a raba Najeriya zuwa shiyya shiyya. Musamman mutanen yankin yarbawa dake kudu masu yammacin kasar nan, idan ka kula da take takensu, zaka gane bukatarsu shine a koma mulkin shiyya shiyya, kamar yadda take a baya a karkashin jagorancin Awolowo.”

  Ango Abdullahi ya cigaba da fadin “kazalika mutanen inyamurai dake yankin kudu maso gabas, na san Cif Alex Ekweme farin sani, kuma shugaba na ne. Ekweme ne ya jagoranci kabilar inyamurai a babban taron majalisar kasa da aka yi a 1995/1996 inda suka bukaci Najeriya ta zauna a matsayin kasa daya al’umma daya, kuma a wannan lokaci ana sa ran yan Najeriya zasu magance matsalolin dake rarraba kawunansu.


  “Amma bukatar tasa bata samu karbuwa tsakanin mahalarta taron, sai gashi daya samu daman sake yin duba ga rahoton kwamitin data bada rahoton taron, sai ya cusa batun a raba Najeriya ta shiyya shiyya, kuma wannan baya cikin tsarin mulkin kasar nan.

  “Mutanen nan suna da son kansu ne kawai, kwadayinsu shine a basu mukaman siyasa ko a nada su manyan kujeru, kuma wannan ba karamin koma baya bane ga cigaban kasar nan.”

  Farfesan bai tsaya nan ba, ya bada dalilinsa na shirin Arewa fita daga Najeriya “alkalumma sun nuna duk sauran yankunan Najeriya suna da bukatar a raba Najeriya a baiwa kowa rabonsa, don haka ban ga dalilin da zai sa Arewa zama a Najeriya. Manyan Najeriya sune ke cin diddigen zaman Najeriya kasa daya, don haka muddin suna jagorantar al’umma a siyasance, toh ba zamu daina samun matsaloli ba, kuma ba zamu taba samun cigaba a haka ba, cigaban da muka san samu tun 1960.

  “Kaga misali Ben Nwabueze, mun sha zama da shi muna tattauna batutuwan da suka shafi kasa, mutum ne daya tsani Arewa, ya tsani Hausa Fulani. Bai isa ya karyata ni ba, saboda ya maimaita haka ba sau daya ba, ba sau biyu ba.”

  Dayake bayani dangane da sake fasalin Najeriya, Ango Abdullahi yace “wani sake fasali kuma kake magana? Bayan a baya muna zaune kasa daya, sai aka raba mu zuwa shiyya shiyya, aka sake raba mu zuwa jihohi daban daban, yanzu kuma aka mayar damu kananan hukumomi guda 774 da sunan a baiwa nakasa daman taka rawa a harkar mulki. Me ya rage?”
  Naij.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: “A shirye muke Arewa ta ɓalle daga Najeriya” – Farfesa Ango Abdullahi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });