'YAN SANDA A JIHAR KANO SUN HARBE WASU 'YAN FASHI HAR LAHIRA


Rundunar ‘yan sandan jahar Kano sun harbe wasu yan fashi da makami guda Biyu a daidai kauyen Kwanar Dangora da ke karamar hukumar Bebeji a jahar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar, DSP Magaji Musa Majiya, shi ya sanar da haka ga manema labarai a jiya Alhamis.
A fadarsa, al’amarin ya faru ne a ranar Laraba a lokacin da yan sandan ke sintiri a hanyar da ta tashi daga Kano zuwa Kaduna da misalin karfe 8:15 na dare, yayin da ‘yan sandan suka yi kicibis da ‘yan fashin a yayin da suka tare hanya suna fashi.
Ya ce, ‘yan sandan sun mayar da martani ne bayan da ‘yan fashin suka bude masu wuta da ganin su.
Biyu daga cikin barayin sun mutu, inda uku kuma suka gudu da raunuka. Haka kuma yan sandan sun samu bindiga daya mallakar barayin da albarusai da wukake da layoyi.

(Al'ummata)
'YAN SANDA A JIHAR KANO SUN HARBE WASU 'YAN FASHI HAR LAHIRA 'YAN SANDA A JIHAR KANO SUN HARBE WASU 'YAN FASHI HAR LAHIRA Reviewed by on January 14, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.