Kowannen mu ya san muhimmancin da ruwa ke da shi wajen tabbatar da
kasancewar mu cikin koshin lafiya, toh sai dai da yawa ba su san adadin
ruwan da ya kamata su na sha ba.
Ko a tsakanin masana, babu daidaito a ra’ayoyin su game da wannan. Yayin da wasu ke ganin kofi 8 a rana ya wadatar, wasu suna ganin mutum na bukatar akalla lita 3 a rana.
Koma ya ya ne dai, jikin mutum kan yi masa nuni idan yana bukatar ruwa ta hanyar jin kishi, bushewar baki, jiri da sauransu. Kuma akwai matukar hatsari idan mutum ya ki la’akari da wadannan alamomi.
Akwai illoli da dama da rashin shan ruwa isasshe ke haifarwa, Kadan daga cikin su sun hada da:
1. Tamushewar fata da saurin tsufa
2. Rashin iya narka da abincin da aka ci da wahala wajen fitar da bahaya
3. Gyambon ciki
4. Rama
5. Ciwon gabobi
6. Zafin jiki
7. Mantuwa da toshewar kwakwalwa
8. Rashin kuzari da saurin gajiya
Da sauransu.
MUJALLARMU

Tags:
FADAKARWA