Gwamnatin Tarayya Ta Daukaka Kara Kan El-Zakzaky

Gwamnatin tarayya ta daukaka karar da ke kalubalantar hukuncin da Mai shari’a Kolawale Gabriel ya yanke da ke bukatar a saki shugaban kungiyar shi’a Sheik Ibrahim El-Zakzaky da matarsa, tare da gina masa gida a kowace jaha da ya so a fadin kasar nan. Hukuncin ya kuma bukaci a biya matarsa diyyar naira miliyan 50.
Hukumar tsaron farin kaya, Ma’aikatar tsaro da ma’aikatar shari’a su suka kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara, da cewar alkalin ya yanke hukuncin ne bisa kuskure saboda ya hada kararraki daban daban a guri guda.
Daukaka karar ta kunshi laifuka 7 na shugaban kungiyar wanda ke tsare tun Disambar shekarar 2015.
A ‘yan kwanakin nan, mambobin kungiyar shi’an sun kara kaimi wajen yin zanga zanga, inda suke kira da a saki jagoran na su.
A zanga-zangar su ta karshe, ‘yan Shi’an sun gamu da fushin ‘yan sanda da su ka yi ta jefa musu barkonon tsohuwa.
ALUMMATA
Gwamnatin Tarayya Ta Daukaka Kara Kan El-Zakzaky Gwamnatin Tarayya Ta Daukaka Kara Kan El-Zakzaky Reviewed by on January 29, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.