HAFSAN DAN SANDA DA 'YAN DABAN SIYASA SUKA FILLE KAN SHI A JIHAR RIVERS

Marigayi DSP Muhammed Alkali dan Arewa jinin Arewa,ya hadu da ajalin shi ne a yayin wani kwanton bauna da wasu 'yan daban siyasa suka yi masu a yayin da suke gudanar da aikin su
.Shi da direban shi an kashe su,sauran jami'ai 5 sun bace ba a gan su ba har yanzu.Wannan al'amarin ya faru ne a karamar hukumar Omoku Onelga ta jihar Rivers a ranar Asaba 10/12/2016.
DSP Muhammad Alkali ya rasu ya bar mata daya da yara biyu sai kuma mahaifin sa wanda tsohon kwamishinan 'yan sanda ne,ciki har da Jihar Lagos.Allah ya jikan wannan bawan Allah.

SHARHI
Lokaci ya yi da zaratan askarawan arewacin kasannan da ke aikin damara a kudancin kasannan su tashi tsaye su sa ido sosai kuma su yi iya abinda ya kamata domin su kare kawunan su daga irin wannan cin zarafi da ake yi masu saboda asalin su na zama 'yan Arewa,idan zaku tuna,a wannan karamar hukuma ne aka kashe wani soja kasa da sati biyu da suka wuce,kana aka kashe jami'an tsaro na NSCDC har guda 10,yanzu kuma ana zaton an kashe 'yan sanda 7 har da marigayi DSP Muhammed Alkali.
Akwai wanda ya gagari hukuma ne? idan babu, yau ya zama wajibi hukumar 'yan sanda ta nuna kwarewar ta wajen ganowa da zakulo wa'yan da ke da hannu a wannan aika-aikan don su fuskanci hukuncin da ya yi daidai da su.Idan kuwa ba haka ba,lallai raini da wulakanci kan jami'an tsaro zai samu gindin zama a wannan yankin,kuma ni na san akwai jami'an tsaro 'yan asalin Arewacin kasar nan da yawa a wannan yankin,ma'ana su ne za a cutar da su idan aka yi sakaci. 

Gida - Leadership Hausa

Assalamu alaikum, Editan LEADERSHIP Hausa mai farin jini, ka bani dama na yi kira ga gwamna Kashim...

Gida

(null)

Labarai, kai tsaye- Radio France Internationale RFI

Samu dukkanin shirye-shiryen RFI Siyasa da Al'adu da Wasanni da Labarai da dumi-duminsu na Afrika da Faransa da duniya.

NIGERIAN NEWSPAPERS

Flash or unlock your phone at SENIORA TECH shop No.51 upstairs.OLUMBO shopping complex Ahmadu Bello way Birnin kebbi. 08062543120 http://...

Wasanni

Domin samun labaran wasanni kai tsaye daga club na kwallon kafa na turai

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN