Yayin da kudirin samar da ‘yan sandan jihohi ya tsallake karatu na biyu, an ba da sabon umarni kan zabar kwamishinan ‘yan sanda. Legit ya wallafa.
Sabuwar dokar da ke neman kirkirar ‘yan sandan jihohi an kawo ta ne saboda dakile matsalar tsaro da ya yi katutu a jihohi.
Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya gana da gwamnonin jihohi kan matsalar tsaron da ta addabe su.
A bangaren nada kwamishinan ‘yan sanda wanda gwamnan jiha zai yi, dokar ta fayyace cewa dole sai da amincewar Majalisar jihar.
Har ila yau, gwamnan ba zai iya nada kwamishinan ba har sai ya samu amincewa daga hukumar ‘yan sanda ta Tarayya.
Dadi da kari, gwamnan jiha zai iya cire kwamishinan ‘yan sanda da amincewar hukumar ‘yan sanda ta Tarayya da kuma amincewar kaso biyu cikin uku na Majalisar jiharsa.
Dokar ta bayyana cewa dole za a kirkiri hukumar ‘yan sanda ta jihohi da za ta rika sa ido a bangarorin aikin dan sanda, cewar Premium Times.
Gwamnan jiha zai iya bai wa kwamishinan ‘yan sanda umarni karkashin doka amma idan ya saba doka kwamishinan zai iya kai kara zuwa hukumar ‘yan sandan jihar.
Har ila yau, Majalisar Tarayya ce za ta rika sabunta kasancewar hukumar ‘yan sandan jihohi duk bayan shekaru biyu don tabbatar da su na kan tsarin doka.
Dokar ta kuma fayyace aikin dan sandan Gwamnatin Tarayya da na jiha musamman a wurin samar da zaman lafiya, cewar Daily Post.
Dokar ta kara da cewa ‘yan sandan Tarayya ba su da hurumin shiga harkokin tsaron jihar har sai gwamna ya bukaci haka ko kuma an samu tabarbarewar tsaro da ka iya jefa jihar cikin wani hali.
From ISYAKU.COM