Shugaba Tinubu ya kori wasu manyan mutane 2 da Buhari ya naɗa, ya faɗi muhimmin dalili


Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tsige wasu manyan hadiman gwamnatin tarayya waɗanda magabacinsa, Muhammadu Buhari ya naɗa.

A rahoton TVC, waɗanda Tinubu ya kora daga aiki sun haɗa da shugaban hukumar FCCPC (Federal Competition and Consumer Protection Commission), Babatunde Irukera. Legit Hausa ya wallafa.

Bayan shi kuma shugaban ƙasan ya tsige darakta janar kuma shugaban hukumar BPE (Bureau of Public Enterprises), Alexander Ayoola Okoh.

Wannan mataki na tsige shugabannin hukumomin biyu na tarayya na kunshe ne a wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban ƙasa, ranar Litinin, 8 ga watan Janairu.

Bayo Onanuga, babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru ya wallafa sanarwan a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Sanarwan ta umarci waɗanda matakin ya shafa su miƙa harkokin mulki ga babban ma'aikacin da ke ƙasa da su a hukumomin yayin da korarsu ta fara aiki nan take.

Manyan ma'aikatan da zasu miƙa wa ragamar hukumomin za su ci gaba da kula da harkokin waɗannan hukumomin har zuwa lokacin da shugaban ƙasa ya naɗa sabbi.

Sanarwan mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ta ce:

"Ana umurtan korarrun shugabannin hukumomi su miƙa ragama ga manyan jami'an gwamnati da ke ƙasa da su a wurin gabanin naɗa waɗanda zasu maye gurbinsu."

Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan shugaba Tinubu ya dakatar da ministar harkokin jin ƙai da walwala, Dokta Betta Edu.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN