Jami'an tsaro na da hannu a kisan kiyashin da ke wakana a Plateau? Gaskiya ta bayyana


Rundunar tsaro Najeriya ta yi martani kan jita-jitar cewa jami'an tsaro sun farmaki Kiristoci a jihar Plateau. Legit Hausa ya wallafa.

Rundunar ta karyata hakan inda ta ce babu kamshin gaskiya tattare da labarin wanda babu wata hujja.


Rundunar ta bayyana haka ne a shafinta na X a yau Alhamis 25 ga watan Janairu kan wannan lamari.

Wannan martani na zuwa ne bayan shugaban kungiyar Kiristoci, CAN a jihar, Rabaran Timothy Daluk ya zargi jami'an tsaro da goyon bayan wani bangare a rikicin.

Rundunar ta ce kawai nema ake yi a bata sunan rundunar tsaron kasar da karairayi marasa tushe da asali cewar ta na kashe Kiristoci.

Ta ce abin takaici ne yadda shugaban CAN da ake zaton koyar da zaman lafiya zai neman ta da zaune tsaye da bata sunan rundunar, cewar TheCable.

Ta bukaci al'umma da su yi watsi da wannan jita-jita inda ta ce har gobe jami'an tsaro ba sa goyon bayan ko wane bangare a rikicin.

Har ila yau, rundunar ta godewa jama'a musamman wadanda su ke bin doka a yankunan tare da ba su goyon baya a kokarin tabbatar da zaman lafiya.

Sanarwar ta ce:

"Mun samu labarin wani faifan bidiyo da shugaban kungiyar CAN a jihar, Rabaran Timothy Daluk ke neman bata sunan rundunar soji.

"Babu kamshin gaskiya a bidiyon da ke zargin jami'an tsaro su na goyon bayan wani bangare a rikicin.

"Abin takaici ne haka ya fito daga shugaban addini da ake tsammani koyar da zaman lafiya, rundunar ba ta goyon bayan ko wane bangare a kokarin tabbatar da zaman lafiya."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN