Har yanzu ba duriyar mutane 12 bayan hatsarin Jirgin rura a Neja, bayanai


Mutane 12 ne har yanzu ba a ji duriyarsu ba bayan hatsarin kwale-kwale a ranar Litinin a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.


 Jirgin ruwan da ya taso daga Durga Mashaya, karamar hukumar Borgu ta jihar, na dauke da fasinjoji kimanin 100.


 Kazalika jirgin na dauke da kaya ya nufi kasuwar Wara da ke jihar Kebbi a lokacin da ya kife saboda tsananin igiyar ruwa da kuma cunkoso.


 Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar wa Daily trust faruwar lamarin a ranar Laraba 17 ga watan Janairu.


 Ya ce baya ga maza uku da mata biyar da suka rasa rayukansu, an samu nasarar ceto wadanda suka jikkata ta hannun tawagar bincike da ceto wadanda suka hada da masu ruwa da tsaki na cikin gida da gaggawar mayar da martani ya rage adadin wadanda suka mutu.  Duk da haka, 12 sun …ďace.


 Ya kara da cewa jirgin mai dauke da fasinjoji 100, ya cika makil da mutane da kayayyaki zuwa kasuwar Wara da ke jihar Kebbi, inda ya kara da cewa, hadarin ya faru ne sakamakon tsananin igiyar ruwa da kuma cunkoso.


 Ya bayyana sunayen wasu da aka ceto da ransu kamar Malama Adama Babangida, Bello Usman, da Bawa Alh.  Ayuba, Danyarbawa Danmanyan, Umaru Alhaji Mainasara, Rufayatu, Ladidi, Abdullahi Abubakar, Isah Suleiman, Rakiya Abdullahi da Sakina Ibrahim.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN