Daga Shu'aibu Mungadi
Wanda bai yi karatu ko na sakandire ba, ya bude chemist a kauyenku har tiyata yake yi, Kana ce masa dafta.
Kabila ne yake maka talla da yaren Hausa, Kuma a saka a gidan radiyon garinku ba ka ce komai ba.
An yi kasafin kudi an tauye yankin ka, wakilinka a majalisa bai ce komai ba, kaima ba ka ce masa komai ba.
An kashe maka mutum dari biyu yau ance kuskure ne, ka yi hayaniyar kwana 3, ka koma ka kwanta, gobe an kara kashe 100, jibi 200, gata 300, abin har yabi jikinka ka yi shuru.
An debi rubabbun ministoci an baka kana murna tunda sun fito daga Yan kin ku,
Wakilanku sun samu dama sun dibga sata sun dawo sun sayi sarauta kana girmama barawo da rawani.
Gwamnan ka ya sace maka biliyan dari, ya maka empowerment na miliyan dari. ka shiga radiyon kana masa godiya.
Ilimin ya tabarbare a yankinku, makaranta primary ta zama wajen kwanan jakai da awakai, amma fa kai Flyover ce matsalarka
Wai dan arewa da yar arewa, wa ya saka maka wannan wawacin?
Daga Shu'aibu Mungadi
From ISYAKU.COM