Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ce za ta dauki mataki kan wani jami’inta da aka kama a na’urar daukar hoto yana neman cin hanci daga hannun wani direban mota.
A cikin wani faifan bidiyo, an ga jami’in da aka bayyana da suna ASP Luka Bashayi da ke aiki a yankin Ogudu yana tambayar wasu masu ababen hawa da su yi wani abu mai ‘sharp sharp’’. Ana kuma iya jin ya ba su sunan bankin da yake amfani da shi.
Da yake mayar da martani ga faifan bidiyon, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce;
''Ba za mu yi watsi da wannan ba. Shi ASP Luka Bashayi, yana aiki a yankin Ogudu.
A halin yanzu, @Lagos_PoliceCRU ya fara aiki akan wannan.''
From ISYAKU.COM