Yan bindiga sun kai sabon farmaki kauyen Sokoto, sun yi mummunar barna


Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu shida a wani hari da suka kai kauyen Tursa da ke karamar hukumar Rabba a jihar Sokoto. Legit ya wallafa.

An kai harin ne da sanyin safiyar Talata.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, Ahmed Rufa’i, maharan sun mamaye kauyen inda suka kona wani gida inda mutum daya ya mutu.

Ya ce an kona wasu kadarori da suka hada da babura yayin da aka kuma sace wasu dabbobi da ba a tantance adadinsu ba, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin farautar wadanda ake zargi da aikata laifin, ya kuma yi alkawarin bayar da karin bayani idan an samu nasara.

Sokoto dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar ‘yan fashin daji da ke kai hare-hare a duk sa'ilin da suka ga dama.

Sauran jihohin sun hada da Kaduna, Kebbi, Zamfara da Katsina.

A wani bangare na matakan da ake dauka kan ‘yan bindiga a yankin, sojojin Najeriya na kaddamar da hare-hare ta sama tare da kashe wasu ‘yan ta’adda da manyan kwamandojinsu.

‘Yan bindiga sun dade suna addabar wasu jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya, inda suke gudanar da ayyukansu daga sansanoninsu da ke a dazuzzukan yankunan.

A hare-haren da suke kai wa kauyukan, suna kwasar ganima da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN