Ta faru: An kama mutane uku da ke tone gawaki a kabari suna sayarwa matsafa sassansu don yin kudi


 Rundunar Amotekun Corps a jihar Osun ta kama wasu mutane da suka kware wajen tono gawarwaki tare da cire sassan jikinsu domin yin tsafi.

 A wata sanarwa a ranar Talata, 12 ga watan Disamba, mai magana da yawun Amotekun na jihar Osun, Adeniyi Adeshola Brown, ya ce mutanen ukun sune;  Kamilu Kehinde mai shekaru 43 mai sana'ar kanikanci da Akeem Hamzat direba mai shekaru 56 da kuma Wakeel Baka mai sana'ar tsibbu.

 Brown ya bayyana cewa an kama su ne biyo bayan bayanan sirri da jami’an rundunar Iwo suka samu.

 Ya ce: “A yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun yi ikirari cewa suna cikin harkar tono gawarwaki daga kaburbura;  wanda sai su sayar wa masu saye da suke bukatarsu domin yin tsafin neman kudi".

 Kakakin, ya bayyana cewa kwamandan rundunar ta jihar Osun, Bashir Abiodun Adewinmbi, ya bayar da umarnin a mika wadanda ake zargin zuwa rundunar ‘yan sandan Najeriya domin gudanar da bincike na gaskiya da kuma gurfanar da su gaban kuliya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN