NDLEA ta gano katafaren gonar da ake noman wiwi a Sokoto, ta cafke mutum daya


Jihar Sokoto - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, shiyyar Jihar Sokoto, ranar Juma'a, ta kama wani Anas Sani, mai shekaru 32, wanda aka gano yana noman tabar wiwi a jihar. 

Babban Kwamandan Hukumar a jihar, Iro Adamu, a bayaninsa, ya ce sun gano haka ne a binciken da aka gudanar daren Juma'ar da ta gabata a yankin Sanyinna da ke karamar hukumar Tambuwal a jihar, bayan samun bayanan sirri. Legit Hausa ya wallafa.

"An shuka tabar ne a gonar masara ta yadda iya kwararru ne kawai za su iya gane menene.

"Ta waje ce mai karfi kuma mai tsada," in ji shi.

Adamu ya ce wannan ne karon farko da aka samu irin gonar a jihar, wanda ya ce, dole a gudanar da gangamin yawan wayar da kai don dakike al'umma daga fadawa haramtattun kasuwanci.

Wanda ake zargin, mai 'ya'ya biyu, da yake zantawa da manema labarai, ya ce ya koyi kasuwancin a Jihar Lagos lokacin da ya ke sana'ar kanti.

"Wannan ne karo na farko. Na koya lokacin ina rayuwa a Lagos sai na yanke shawarar yi a garinmu Sayinna.

"Babban yayana yayi bakin kokari kar na yi amma banji shawara ba.
"Nagode Allah da aka kama ni kafin in fara cin riba.

"A shirye nake na karbi hukuncin abin da na aikata saboda ya zama izna ga masu sha'awa nan gaba," in ji shi

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN