Gwamnatin Bayelsa ta yi martani kan auren yar shekara 4 da dan shekara 54 a jihar



Gwamnatin jihar Bayelsa ta sanya baki a haramtaccen auren da aka yi wa wata yarinya yar shekara hudu da wani dattijo dan shekara 54 a garin Akeddei, karamar hukumar Sagbama ta jihar. Legit Hausa ya wallafa.

Gwamnatin Gwamna Douye Diri ta gayyaci iyayen karamar yarinyar da kuma mutumin mai shekara 54 bayan auren ya yadu a shafukan soshiyal midiya, rahoton Premium Times.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da ma’aikatar harkokin mata, yara da ci gaban al’umma ta saki.

Gwamnatin jihar mai albarkatun man fetur ta ce auren ya saba wa adalci, daidaito da kuma sanin yakamata.

A cewar jaridar New Telegraph, basaraken ya amsa gayyatar da gwamnati ta yi masa, kuma ya yi alkawarin gabatar da yarinyar, iyayenta, angon, shugaban matasa da kuma shugaban kwamitin ci gaban al’umma na yankin.

Gwamnatin jihar ta ce bata goyon bayan auren kananan yara da sunan al'ada.

"Wannan ne dalilin da yasa gwamnatin jihar ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen amincewa da dokar kare hakkin yara ta jihar Bayelsa.

"Muna daukar matakai don kubutar da yarinyar daga dukkan masu alaka da wannan haramtaccen biki da suka yi wa lakabi da "al'amari na tsarkakewa kawai."

Gwamnatin ta kuma ce tana aiki tare da rundunar yan sandan jihar Bayelsa, don tabbatar da ganin irin haka bai sake faruwa ba a jihar.

A baya mun ji cewa al’ummar kauyen Akeddei da ke karamar hukumar Sagbama a jihar Bayelsa sun shiga rudani bayan aurar da wata yarinya ‘yar shekara 4 ga wani dattijo.

Iyayen yarinyar ne suka ba da auren yarinyar wacce ba a bayyana sunanta ba ga dattijo dan shekara 54 wanda hakan ya jawo cece-kuce a yankin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN