Abdul Haseer wanda ya shahara da suna Malam Ali a shirin Kwana casa’in, ya koka game da dakatar da shi da aka yi daga harkar fim. Legit Hausa ya wallafa.
A bidiyon da Abdul Haseer ya fitar a dandalin sada zumunta wanda mu ka ci karo da shi a Twitter, ya aikawa Gwamna Abba Kabir Yusuf sako.
Jarumin ya sanar da Mai girma Abba Kabir Yusuf cewa an yi masa hukunci wanda a cewarsa, ya saba ka’ida yana kokarin jan hankalin mata.
Abdul Haseer ya ce burinsa shi ne ganin ya wayar da kan matasa musamman mata, a karshe sai hukumar tace fina-finai ta zarge shi da batsa.
Jawabin Malam Ali zuwa ga Gwamna Abba
"Babu wani mahaluki mai hankali wanda zai zo ya ga ‘yarsa, matarsa, kanwarsa ko kuma yayarsa suna rawan zubar da mutunci, suna sa damammun kaya a shafukan sada zumunta, musamman kafa ta Tik Tok.
Ya Mai girma Gwamnan jihar Kano, wannan dalili ya sa na ke amfani da hanyoyi dabam-dabam wajen ganin cewa na jawo hankalin matasanmu da ni kai na, musamman ‘ya ‘ya mata da yakana, alkunya da kamun kai.
Ya Mai girma Gwamnan jihar Kano, ina tura sakonnina ba tare da cin mutunci ga addina ko jihar Kano. A matsayinka na uba a jihar Kano, ina so in yi amfani da wannan damar in fada maka cewa an dakatar da ni daga shirya fina-finai a masana’antar Kannywood na shekara biyu ba tare da ka’ida ba." -
Mutuminnan sai magana yake
— purpleberry 🍇🍇 (@Ameenertu_) November 15, 2023
Baiji kunyar yada alfasha ba a kwanakin baya
Naji dadi sosai da suka koreshi
YAnzu kuma yazo da wata sabuwa 😀😃😃 pic.twitter.com/apLzxm8LiO