An kai hari a safiyar Lahadi kan wani dakin ajiyar makamai na sojoji a Freetown babban birnin kasar Saliyo, a wani yunkurin juyin mulki gwamnatin kasar ta yi zargin an yi, yayin da ta sanya dokar hana fita a fadin kasar nan take.
Gwamnati ta ce an dakile wadanda suka yi yunkurin kutsawa cikin rumbun ajiyar makamai a wani babban barikin sojoji, amma an bukaci jama’a su zauna a gida.
Shaidu sun ce sun ji karar harbe-harbe da fashe-fashe a gundumar Wilberforce a birnin, inda aka ajiye makaman yaki kuma mazaunin wasu ofisoshin jakadanci a babban birnin kasar.
Wasu shaidun gani da ido sun ce sun ji ana musayar wuta a kusa da wani barikin sojin ruwa a gundumar Murray a Freetown.
From ISYAKU.COM