An yi musayar wuta tsakanin 'yan sanda da sojoji, an kashe wani sufeta a Adamawa


Shelkwatar 'yan sanda a jihar Yola a sanyin safiyar yau ya zama tamkar filin yaki, inda sojoji makare a motoci 12 suka bude wuta, har suka kashe sufetan 'yan sanda, Jacob Daniel. Legit Hausa ya wallafa.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Afolabi Babatola ya yi Allah wadai da irin wannan farmakin da sojojin suka kai wa 'yan sanda, ya kuma gargade su kan kiyaye faruwar hakan nan gaba.

Sojoji da 'yan sandan, sun yi arangamar ne a sha tale-talen Target, karamar hukumar Yola ta Arewa, lamarin da ya jawo asarar ran sufetan 'yan sanda Daniel.

The Tribune ta ruwaito cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, ya bayar da umurnin gudanar da bincike, don wanzar da zaman lafiya da yin adalci.

Kwamishina Babatola ya yi gargadin cewa kai wa kowanne jami'i farmaki yayin da yake a bakin aiki babban laifi ne, kuma hukumar ba za ta lamunci hakan ba.

Da ya ke ba da tabbacin yadda hukumar ta ke martaba rayuwar jami'anta, kwamishinan ya ce dole za su bi matakan doka don bin kadin jami'in da aka kashe, The Leadership ta ruwaito.

Da 'yan jarida suka tuntubi kwamandan bataliyar soji ta 23, Birgediya Janar Gambo Mohammed kan lamarin, ya ce su jami'an 'yan sanda ne suka harbi wani soja tare da boye shi, wannan ya sa sojojin suka je karbo shi.

Sai dai wani jami'in dan sanda ya shaidawa Tribune cewa an garzaya da wani jami'in soji sanye da kayan gida zuwa asibitin Modibbo Adama da ke Yola.

Ya ce ba su boye jami'in da aka ji wa rauni ba, sabanin ikirarin da hukumar 'yan sandan ta ke yi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN