An gano matar aure da ke hada yan mata da maza suna lalata a gidanta kan gadonta na aure don kudi a Badariya jihar Kebbi


Wata matar aure (an sakaya sunanta) wacce ake zargin tana amfani da gidan aurenta wajen hada yan mata da maza domin yin lalata a gadonta na aure ta shiga hannu a Birnin kebbi.


 Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com  ya tattaro cewa jami'an aikin tsaro na sa kai, a karshen makon da ya gabata, sun kama wasu yara, maza biyu da mata biyu a unguwar Gesse phase 1 da misalin karfe 1:30 na dare kan hanyarsu ta zuwa gidan rawa.  Binciken da jami’an suka gudanar domin gano ko su waye ne yaran ya kai su wajen matar a unguwar Badariya, bayan daya daga cikin yarinyar ta ce matar ce mai kula da ita.


 Rahotanni sun bayyana cewa jami’an a yayin bincikensu na farko sun gano cewa yarinyar ta bar gidan iyayenta a Birnin kebbi kimanin wata guda da ya gabata, kuma tun daga lokacin ne iyayen ke neman ta.


 Har ila yau, bayanai sun nuna cewa matar ba ta musanta ba bayan yarinyar ta yi zargin cewa ita ce ke ba ta masauki lokaci zuwa lokaci har da wata kawarta kuma takan hada su da maza don yin jima'i a É—akinta a kan gadonta na aure don neman kuÉ—i.


 A ranar 24 ga watan Oktoba, 2023 ne jami’an suka kai matar zuwa ofishin ‘yan sanda Area command Birnin kebbi domin yi mata tambayoyi, inda aka ce ta yi ikirari da alakanta kananan ‘yan mata da maza domin yin lalata a dakinta na haya, kan gadon aurenta. 


 An ce mijin ya san abin da matarsa ​​ke yi ne a karon farko a gidansu a ofishin ‘yan sanda, lokacin da matarsa ​​ta yi ikirari cewa tana alakanta ‘yan mata da maza domin yin jima’i a cikin dakinsu, kuma a kan gadon aurensu.


 Har ila yau, an tattaro cewa matar ta sanya hannu a ofishin rundunar ‘yan sanda cewa kada ta sake yin irin wannan aiki, sakamakon rashin sha’awar ci gaba da shari’ar daga jami’an aikin sa kai na tsaro da suka kawo ta ofishin yan sanda.


 Da aka tuntubi Daraktan Shari’a na hukumar HISBAH na jihar Kebbi, ya ce ba a tuntube su a hukumance ba kan lamarin.


 Wata majiya a Sashen Tsaro na Cabinet Offis Birnin kebbi, ta shaida wa jaridar cewa sashen na sane da lamarin.


 Jami’in hulda da jama’a na Rundunar yan sandan jihar Kebbi ya yi alkawarin zai tuntube mu kan lamarin bayan gabatar masa da zancen.  Amma bai mayar da martani kan tuntubar da aka yi masa na karshe ba kafin buga wannan rahoto.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN