Yadda ni da Obasanjo muka yi wa gwamnoni 5 magudi aka amshe kujerunsu a 2003 – Atiku


Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben 2023, Alh Atiku Abubakar, ya yi fallafa yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, cewa shi da tsohon maigidansa, Cif Olusegun Obasanjo sun yi magudin zaben 2003 a Kudu maso Yamma domin maye gurbin Gwamnonin Jihohin da ‘Yan Takarar PDP.

 Atiku ya bayyana haka ne a wajen taron yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai cewa shi ne ya ceci Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu, wanda yanzu shi ne Shugaban Najeriya, daga karbe kujerarsa kamar sauran Gwamnoni a yankin. PM News ta rahoto.

 Atiku ya bayyana cewa a lokacin shugaba Obasanjo ya so jam'iyyar PDP ta karbe jihohin Kudu maso Yamma amma Atiku ya dage cewa a bar Legas.

 "Na ce, bar Legas kadai," in ji shi.

Ku tuna cewa jihohin Legas, Ogun, Oyo, Osun, Ondo da Ekiti gwamnonin jam’iyyar adawa ta AD, Sanata Bola Ahmed Tinubu, Aremo Segun Osoba, Alhaji Lam Adeshina, Cif Bisi Akande, Cif Adebayo Adefarati da Chief  Niyi Adebayo, su ne Gwamnoni a jihohinsu na Yammacin Najeriya kafin harin Obasanjo/Atiku kan dimokuradiyya wanda ya sa duk gwamnonin da aka ambata aka fitar da su daga kujerunsu, sai Bola Tinubu na Legas kadai ne ya rage a lokacin.

 Wannan tonon sililin ya tunatar da ‘yan Najeriya irin kazamin siyasa da za a yi a zaben 2023 karkashin sa idon Obasanjo da Atiku.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN