Al’ummar garin Amukpe da ke karamar hukumar Sapele a jihar Delta sun shiga cikin tashin hankali bayan da aka tsinci gawar wani yaro da ake kyautata zaton bai kai shekara 10 da haihuwa ba, a wata rijiya da aka yi watsi da ita.
An tattaro cewa wani magidanci da ke kusa da ya rika amfani da rijiyar wajen wanke motarsa ya gano wannan mumunar lamari da daddare.
A cewar wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa, mutumin yana diban ruwa a rijiyar kamar yadda ya saba sai ya ji wani abu ya rike guga.
Da ya haska cikin rijiyar da fitilar tocila, sai ya ga gawar wani yaro yana shawagi a cikin ruwan.
“Nan da nan ya yi kururuwa, wanda ya ja hankalin sauran mazauna wurin zuwa wurin rijiyar. Tuni dai gawar ta fara rubewa,” in ji ganau.
An sanar da ’yan sanda, kuma nan da nan suka garzaya zuwa wurin.
Daga bisani an cire gawar daga rijiyar kuma an ajiye ta a dakin ajiyar gawa domin a tantance gawar.
Duk kokarin da ‘yan sanda suka yi na game wadanda ya mutu da kuma gano ‘yan uwansu ya ci tura har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, domin babu wanda ya gane yaron a cikin al’umma, haka kuma ba a samu rahoton wani mutum da ya bata a baya ba.
Yunkurin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, Edafe Bright ya ci tura, sai dai wata majiyar tsaro da ba ya son a ambaci sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an fara gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwar da kuma ko wanene mamacin.