Kamfanin simintin BUA, wanda shine kamfanin siminti mafi girma na biyu a kasuwar Najeriya, ya sanar da rage farashin buhun siminti zuwa N3,500. Legit Hausa ya wallafa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba, kamfanin ya ce sabon farashin zai fara tasiri daga ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba.
Farashin buhun siminti a yanzu haka kafin fitar da sanarwar ya kai kimanin N5,000 kowani buhu daya.
Kamfanin BUA wanda yake mallakin attajirin dan kasuwa AbdulSamad Rabiu, ne yana da kayan aiki da ke iya samar da siminti tan miliyan 11.
Za mu zuba ido kan yadda dillalai ke siyarwa jama'a kaya, BUA
Kamfanin ya kuma sanar da cewar duk wadanda suka riga suka biya kudin kaya a tsohon farashi da ba a kai masu ba za su ci gajiyar wannan ragi da aka yi daga ranar 2 ga watan Oktoban 2023.
Ya kuma yi kira ga dillalai masu lasisi da su tabbatar da ganin cewa masu siyan kaya a hannunsu sun ci gajiyar wannan raji da kamfanin ya yi inda ya sha alwashin sanya idanu don tabbatar da ganin an bi tsari wajen siyar da simintin.
DAGA ISYAKU.COM