Da duminsa: budurwa ta yi mutuwar gaggawa lokacin jima'i da saurayi a dakin masaukin baki a birnin Ilori jihar Kwara


Wata budurwa ta mutu suna tsakar jim'ai da saurayinta a dakin masaukin baki a birnin Ilori da ke jihar Kwara.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a gidan baki da ke unguwar Temidire, unguwar Tashar motar Offa a Ilori ranar Litinin, 30 ga Oktoba, 2023.

 Mambobin al’ummar sun yi ikirarin cewa mutumin, wanda ke da shagon aski, yana shan miyagun kwayoyi ne da nufin burge budurwar tasa kafin al’amura su kara tabarbarewa, inji rahoton Nigerian Tribune.

 "Yarinyar ta gaji a lokacin jima'in amma ya zake mata, daga baya ta mutu," wata majiya ta shaida wa jaridar.

 Majiyar ta ce Majiyar ta ce mutumin ya tayar da hankali lokacin matar ta sume kuma hakan ya jawo hankalin ma’aikatan gidan baki.

 An garzaya da matar zuwa wani asibiti da ke kusa inda aka tabbatar da mutuwar ta.

 Mai masaukin baki ne ya kai rahoton faruwar lamarin a ofishin ‘yan sanda ‘A’ Division, Ilori kuma sun kama wanda ake zargin.

 Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, ya ce an kama mutumin.

 "Rundunar 'yan sandan jihar ta kama mutumin da ke da hannu a ciki yayin da aka fara cikakken bincike don sanin hakikanin abin da ya faru tsakanin mutumin da marigayiuar," in ji PPRO.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN