Zamanin da ya fi samun nasarar tattalin arziki a Najeriya shine lokacin Obasanjo, El-Rufai ya bada daliliTsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce wa'adin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya samu mafi nasara ta fuskar bunkasar tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da saukin hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.

 Obasanjo ya mulki kasar daga 1999 zuwa 2007, a matsayin zababben shugaban kasa na farko a jamhuriya ta hudu. Daily trust ta rahoto.

 El-Rufai wanda ya rike mukamin minista a karkashin Obasanjo, ya ce Najeriya, kasa mafi yawan al’umma a Afirka, ta samu ci gaban tattalin arziki a wa’adinsa na biyu daga 2003 zuwa 2007.

 Tsohon gwamnan ya ce Najeriya ta koma “tsari mai inganci kuma mun samu sa’a” a lokacin.

 Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a yayin wani zama a taron Africa In the World a birnin Stellenbosch na kasar Afrika ta Kudu, yayin da ya bayyana bukatar samar da ingantaccen tsari don taimakawa ci gaban tattalin arzikin kowace kasa.

 "Muna da kwamitin tsare-tsare a Najeriya amma bai yi tasiri ba."

 “Idan aka dubi yanayin tattalin arzikin Najeriya, shekaru hudu zuwa biyar mafi nasara na bunkasar tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da rage hauhawar farashin kayayyaki shine lokacin wa’adin mulkin shugaba Obasanjo na biyu a shekarar 2003 zuwa 2007, inda a karon farko,  kasar ta koma cikin ingantaccen tsarin hadaka kuma mun samu sa'a," in ji shi.

 “Farashin man fetur ya fara hauhawa amma ba mu yi kasa a gwiwa ba saboda mun shirya.  Muna da asusun danyen mai da ya wuce gona da iri (ECA) wanda ya dogara ne akan dokar kasafin kudi cewa duk wani rarar da aka samu sama da wani takamaiman farashin danyen mai yana zuwa asusun ajiyar.

 "Kuma da wannan, mun sami damar kawar da duk basussukan da muke bin kasashen waje."

 El-Rufai ya ce karfin kasafin kudin Najeriya ya kasance mafi kyawu a cikin 2007, kamar yadda lokacin da rikicin kudi ya faru a duniya a 2008, "Najeriya ba ta ji komai ba".

 “Ba a ji komai ba a Najeriya saboda Najeriya na da babban asusun ajiyar kudi;  muna da tanadi mai yawa kuma mun sami damar shawo kan lamarin ba tare da wata matsala ta cikin gida ba sabanin yawancin kasashe," in ji shi.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN