MNPP ta kori Kwankwaso daga jam'iyyar nan take


Kwamitin zartaswa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta kori dan takararta na shugaban kasa a zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, Rabi'u Kwankwaso, sakamakon kin bayyana gaban kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar.


 Idan ba a manta ba Majalisar Zartarwar Jam’iyyar ta kasa ta kafa kwamitin ladabtarwa inda ta umarce ta da ta gayyaci Kwankwaso domin ya kare zarge-zargen cin hanci da rashawa na jam’iyyar da kuma karkatar da kudaden jam’iyya/kamfen cikin kwanaki biyar.  Kwamitin ta yi gargadin cewa rashin bayyana gaban kwamitin ladabtarwa, zai sa a kori Kwankwaso daga jam’iyyar kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar 2022 ya tanada (kamar yadda aka gyara).


 Saboda rashin gurfana a gaban kwamitin, jam’iyyar a wata sanarwa da Abdulsalam Abdulrasaq, mukaddashin sakataren yada labaranta na NNPP ya fitar a ranar Talata, 5 ga watan Satumba, ta ce jam'iyyar ta kori Kwankwaso cikin gaggawa saboda ya ki girmama gayyatar kwamitin.


 " Kwamitin zartarwa ta NNPP ta kasa ta yi zaman gaggawa a ranar Juma’a, 1 ga watan Satumba inda ta dauki mataki kamar haka.

 Bayan kin bayyanar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a gaban kwamitin ladabtarwa da ya zauna a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta bayan an gayyace shi a rubuce, an kore shi daga jam’iyyar NNPP nan take.

 Cewa za a kai rahoton tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ga wuraren da suka dace domin amsa tambayoyi kan zargi da suka shafi almubazzaranci da dukiyar al’umma.”

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN